Ad Code

Gwamnatin Jigawa Zata Dauki Karin Malaman Makaranta Dubu Biyu Aiki Karkashin Shirin Koyarwa Na J-Teach.

 


Shugaban kungiyar malamai na jiha, Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio Jigawa na mako mako mai suna Fitila

 

Yace hakan na daga cikin kudirin gwamnatin jihar Jigawa na cike gurbin malaman makaranta da suka yi ritaya da kuma daukar kwararrun malamai aikin koyarwa.

 

Comrade Abdulkadir Yunusa Jigawa ya kara da cewar gwamna Muhammad Badaru ya bada tabbacin mayarda malaman j-teach 400 zuwa 800 zuwa cikakkun malamai na dindindin

 

Ya kara da cewar malaman makaranta dari tara ne suka yi ritaya a jihar Jigawa daga watan janairu zuwa watan da muke ciki.

 

Comrade Abdulkadir Jigawa yana mai cewar gwamnatin jiha da sauran hukumomin bada tallafi na duniya sun bullo da matakai na kara inganta alamurran ilmi.

 

Yace kungiyar malamai ta Jigawa ta gamsu da yadda gwamnati ke kula da harkokin ilmi, musamman a bangaren gine gine da samarda kayayyakin koyo da koyarwa da kuma yiwa malamai Karin girma.

 

Comrade abdulkadir Jigawa yace a nata bangaren kungiyar zata raba dashen Darbejiya dubu daya domin dasawa a makarantu da nufin samar da mahalli mai kyau a makarantu

 

Jigawa State Radio – Facebook Page

Close Menu