Ad Code

APC ta cire mutum 10 daga cikin 'yan takararta a zaben fitar da gwani




Kwamitin tantance ƴan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya zubar da mutum 10 daga takarar zaɓen fitar da gwanin da za a yi a mako mai kamawa.

Shugaban kwamitin John Oyegun ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Juma'a 3 ga watan Yunin 2022 yana mai cewa mutum 13 kawai jam'iyyar ta tantance.

A cewar Oyegun, APC ta tantance mutum 13 ne daga cikin 23 da suka sayi fom suka tsaya takarar.

Ya ƙara da cewa ƴan takarar da ke da sauran jini a jika kawai ne suka haye tantancewar.

Sai dai da aka tambaye shi ko su waye waɗanda aka cire ɗin, Oyegun ya ƙi bayyana sunayensu.

Amma ya ce jam'iyyar za ta sake tantancewar don sake rage ywan ƴan takarar.

Ana sa ran waɗanda aka tantance ɗin za su fafata a takarar zaɓen fitar da gwanin da za a yi a ABuja daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni.

Sai dai Oyegun bai sani ba ko an kai ga tantance tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ko ba a yi ba.

Ya ƙara da cewa ba aikin kwamitin ba ne sanar da sakamakon tantancewar, mutanen da suka tura su haɗo rahoton tantancewar ne za su dawo musu da bayanin da ke akwai.

Ko maslaha APC za ta yi?

Shugaban APC Odigie Oyegun ya ce shugabannin jam'iyyar ne za su shawarta ko zaɓe za a yi ko kuma maslaha za a cimma a zaɓen fitar da gwanin, shi kwamiti aikinsa kawai shi ne ya sanar da jam'iyyar waɗanda aka tantance.

Ya ƙara da cewa "mulkin ƙasa ba ƙaramin aiki ba ne, sai ka yi nazari kan asalin kowa, ka kalli manufofinsu, da irin rawar da suka taka a siyasar Najeriya.

Ƙwarewarsu ce za ta ba su damar taimakon ƙasar da ciyar da ita gaba. "

BBC Hausa

Close Menu