Ad Code

Gwabnatin Nigeria Ta Kayyede Adadin Kudaden da Za’a Iya Cirewa a Bankuna da POS Daga 9 January, 2023

 


Gwabnatin Nigeria Ta Kayyede Adadin Kudaden da Za’a Iya Cirewa a Banki da POS a Kullun (Daily) Dakuma duk Sati (Weekly) Daga 9 January, 2023

Ayau ne Tara ga Watan Nuwamba Dubu Biyu da Ashirin da Biyu (9/11/2022) Gwabnatin Nigeria ta Kayyade adadin kudin da ‘yan kasar zasu iya fitarwa daga asusun su na ajiya a Bankunar Kasar dama wajen masu POS. Kudaden da’aka kayyade wa Bankunan da wajen masu POS din sun hada kamar haka:


1. Kudin da mutum zai iya cirewa a kullun ta POS shine Dubu Ashirin (#20,000)

2. Kudin da mutum zai iya cirewa a acikin Banki shine Dubu Dari (#100,000) duk sati (weekly).

3. Kudin da za’a iya cirewa a acikin Bankuna shine Dubu Dari (#500,000) duk sati (weekly) ga masu gamayya/hadaka na asusun ajiya wato corporate account

Dukkanin Kudin da za’a cire a Banki wanda yawansa yafi yadda Gwabnatin ta Kayyade to akwai charges kamar haka:

1. Asusun ajiya na mutum daya za’a chajeshi kashi biyar na kudaden da zai cire wato 5%. Misali idan zaka/ki cire Dubu Dari Biyar (#500,000) to za’a chaje ka/ki Dubu Ashirin da Biyar (#25,000)

2. Asusun ajiya na gamayya/hadaka za’a chajesu kashi Goma na kudaden zasu cire wato 10 %. Misali idan zasu cire Dubu Dari Biyar (#500,000) to za’a chajesu Dubu Hamsin (#50,000)

Close Menu